Wani fitaccen jagoran ’yan bindiga a Jihar Kaduna, Kachalla Tukur Sharme, ya gamu da ajalinsa a rikicin da ya barke tsakanin kungiyoyin ’yan ta’adda masu gaba da juna.
Kachalla Tukur Sharme shi ne wanda ya jagranci sace dalibai 121 daga makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke Kujama a ranar 5 ga Yuli, 2021.
Shi da yaransa da dama sun sheka lahira ne a wani ƙazamin fada tsakaninsu da abokan gabansu ’yan bindiga a Dajin Rijana da ke Jihar Kaduna, a cewar kwamishinan tsaro, Samuwal Aruwan, a ranar Litinin.
Kwamishin ya ce an kashe ’yan bindiga biyu daya bangaren, a musayar wutar wadda majiyoyin leken asiri suka ruwaito cewa ’yan bindiga biyar sun jikkata, kuma a halin yanzu suna buya a yankin, inda suke neman agajin jinyar raunukan da suka samu.
- Bidiyon Tsiraici: Hafsat Baby ta shiga hannun hukumar Hisbah
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 8, sun ceto mutum 16
- Ambaliya: WHO ta tallafa wa Borno da kayan rigakafin cututtuka
“Sharme, wani dan bindiga da ya garkuwa da daruruwan mutane, ya kuma yi awon gaba da shanun da ba za su kirgu ba, amma ya gamu da ajalinsa a yakin da aka yi tsakanin kungiyarsa da wasu ’yan fashin daji.
“Rikicin ya faru ne a karshen mako a wani wuri da ake kira ‘Hambakko’, a cikin Dajin Rijana da Kaso, wanda ya hada da Kachia da wasu sassan kananan hukumomin Chikun da Kajuru,” inji shi.
Aruwan ya kara da cewa, Sharme ya sha guje wa jami’an tsaro da kyar, kuma ana nemansa ruwa a jallo kafin a harbe shi har lahira.
Kwamishinan ya kara da cewa, Sharme da yaransa ne ke da alhakin kai hare-hare, kashe-kashe, da kuma garkuwa da mutane a yankunan Millennium City, Maraban Rido, Kujama, Kajuru, Maro, da kauyukan da ke yankin Kateri, da kuma wasu kananan hukumomin Kagarko, Kachia da Birnin Gwari.
Har ila yau ayyukan ta’addancin da ya aikata sun tsallaka har zuwa jihohin Katsina da Nijar da ke makwabtaka da Kaduna, wadanda su ma suke fama da ta’addanci.
Ya bayyana cewa daya daga cikin munanan ayyukan da Kachalla Sharme akwai sace dalibai 121 daga makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke Kujama a ranar 5 ga Yuli, 2021.
Ya kuma gargadi mazauna garuruwan Rijana, Kaso, Kasarami, Jaka da-Rabi, Kajuru, da kuma Dutse da kada su taimaka wa duk wani mutum da ke dauke da raunin harbin bindiga.
Ya bukace su da su tuntubi jami’an tsaro mafi kusa ko kuma su isa dakin aikin tsaro na jihar Kaduna.