✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe hakimi da dansa a Kudancin Kaduna

Mahara sun kai hari Masarautar Atyap, Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna, suka kashe Hakimin Gidan Zaki, Mista Haruna Kuyet da dansa, yayin da…

Mahara sun kai hari Masarautar Atyap, Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna, suka kashe Hakimin Gidan Zaki, Mista Haruna Kuyet da dansa, yayin da matarsa ta samu mummunar rauni.

Majiyar Aminiya ta ce maharan sun kawo harin ne da misalin karfe 12 na daren Litinin, kuma ba su zame ko’ina ba sai gidan hakimin inda suka yi nasarar kashe shi tare da daya daga cikin ’ya’yansa yayin da matarsa ke kwance a asibiti don samun kulawa ta musamman.

Yayin da yake bai wa manema labarai tabbaci a kan lamarin, Sakataren Karamar Hukumar Zangon Kataf, Mista Elisha Sako, ya yi tir da ’yan bindigar da suka kai harin.

Ya ce tuni jami’an tsaro suka isa wurin suna kokarin kwantar da hankalin al’umma da kuma gano wadanda suka yi aika-aikar.

Aminiya ta ruwaito cewa harin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati da Masarautar Atyap da wasu kungiyoyi masu zaman kansu ke gudanar  da tarukan zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin mazauna yankin da mabiya addinai daban-daban.