Sakataren Kungiyar Miyetti Allah na Kasa, Baba Othman Ngelzarma, ya ce an kashe mutum 16,830 na al’ummar Fulani makiyaya ciki har da mata da yara kanana a fadin Najeriya tun daga farkon shekarar nan kawo yanzu.
Ngelzarma ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, babban birnin kasar.
- Shin da gaske baraka ta kunno kai tsakanin Buhari da Tinubu?
- Wata mata ta sayar da ’ya’yanta biyu a Ogun
A cewarsa, Shugabanin kungiyar daga dukkan jihohi 36 na kasar da babban birnin tarayya, sun gudanar da wani taro a Abuja a ranar 10 da 11 ga watan Yuni inda suka tattauna batutuwan tsaro da tattalin arziki da ma abin da ya shafi jin dadin al’ummar Fulani makiyaya.
Ya ce taron ya yi nazari tare da nuna bacin rai kan yadda ake ci gaba da kashe al’ummar Fulani da fatattakarsu daga muhallansu a wasu yankunan kasar nan.
“Taron ya nuna matukar damuwa kan yadda ake kai wa al’ummar Fulani makiyaya hari musamman mata da yara kanana wanda kungiyoyin sa-kai da ke samun goyon bayan gwamnaocin jihohinsu da ’yan banga da ma wadansu baragurbi da ke kafa shingen bincike domin gano makiyayan tare da kashe su a wasu sassan kasar nan.
Miyetti Allah ta ce an sace shanun makiyayan fiye da 164,000 da kudinsu ya kai biliyan N10 a fadin kasar nan.
“Har wa yau, taron ya jajanta wa iyalai da dangin Fulani makiyayan da aka kashe a baya bayan nan a sassan kasar ciki har da mata da yara kanana 21 da aka kashe a kauyen Hwkuzu cikin Karamar Hukumar Oyi a Jihar Anambra da ma kisan mummuken da aka yi wa shugabannin kungiyar guda biyar a jihohin Nasarawa da Kogi da Neja da Adamawa,” inji Sakataren.
“Fulani makiyaya su ma fa ’yan Najeriya ne, ba baki ba ne suna da abin tabukawa wajen gina kasar nan,” inji shi.
Ya bukaci gwamnatoci a dukkanin masu ruwa da tsaki da su samar wa da makiyayan da aka raba da muhallansu kayayyakin tallafi cikin gaggawa.
Ya kuma nemi gwamnatocin jihohi da su sake duba kan dokar hana kiwon sake da idon basira domin maye gurbinta da wata mai ma’ana.