✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe dan sanda a harin da aka kai ofishin INEC a Enugu

INEC dai na ci gaba da fuskantar hare-hare yayin da ake tunkarar zaben 2023.

Wasu masu tayar da zaune tsaye sun kai hari ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Karamar Hukumar Enugu ta Kudu a Jihar Enugu.

Kwamishinan Hukumar reshen jihar, Dokta Chukwuemeka J. Chukwu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce maharan sun kashe dan sanda daya tare da kone ofishin.

“Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 9.12 na daren jiya Lahadi 15 ga watan Janairu, 2023.

“A cikin ‘yan sanda biyu da ke tsaron wajen, daya daga cikinsu ya rasa ransa yayin da daya ya samu rauni.

“INEC ta yi addu’ar Allah ya jikan dan sandan da ya rasu ya kuma ba wanda ya jikkata lafiya. Kuma yanzu haka jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike kan harin,” in ji shi.

Ya kara da cewa, an yi nasara maharan ba su shiga cikin ofishin ba, sakamakon daukin gaggawa da jami’an ‘yan sanda da na ssojoji daga shiyya ta 82 suka kai yankin.

Ya kuma ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya bai wa jami’an tsaro umarnin tabbatar da gano maboyar da maharan suka shiga.

Ya ce, “Bugu da kari kuma, an kira taron kwamitin tuntuba tsakanin hukumomi kan harkokin tsaro (ICCES) a Jihar Enugu wanda Kwamishinan INEC da Kwamishinan ‘yan sanda suka jagoranta domin tattaunawa matakan tsaro inganta a lokutan zabe.”

Ya ce za a sake gina ginin da maharani suka latata, kuma hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da shirye-shiryen zaben 2023 a Jihar Enugu da ma kasar nan baki daya kamar yadda aka tsara.

INEC dai na ci gaba da fuskantar hare-hare yayin da ake tunkarar zaben 2023.

A makon da ya gabata, hukumar ta yi gargadin cewa babban zaben kasar nan na iya fuskantar barazanar sokewa idan ba a magance matsalar tsaro yadda ya kamata ba.

Ana zargin haramtacciyar kungiyar ‘yan awaren (IPOB) da kai hare-hare a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.