Rundunar sojin sama ta ƙasa ta kashe ƴan fashin daji 22 yaran marigayi Abdulkareem Boss a jihar Katsina.
Dakaraun Operation Hadarin Daji ne suka kai hare-haren a Batsari da Sola Poli II dake ƙananan hukumomin Batsari da Jibia.
Majiyar Aminiya ta ce ƴan fashin da aka harbe su ne ke kai hare-hare tare da garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Ƙanƙara.
’Yan fashin daji sun kashe ’yan uwan juna biyu a Kaduna
An kwato shanu kusan 800 daga ’yan fashin daji a Kaduna
A ranar Agusta 6, 2022 ne rundunar sojin sama ta ƙasa ta hallaka Abdulkareem Boss da wasu daga cikin yaransa a Dajin Rugu dake jihar Katsina.
Marigayi Abdulkareem Boss ne ake zargi da kisan kwamanda shiyyar Dutsin-ma na rundunar ƴan sanda a ranar Yuli 5, 2022.
Kakakin rundunar sojin sama, Air Commodore Edward Gabkwet ya tabbatar da kashe ƴan fashin dajin sai dai bai bada bayanin farmakin ba.