✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwato shanu kusan 800 daga ’yan fashin daji a Kaduna

Jami'an tsaro ne suka kwato su bayan sun fatattaki barayin

Jami’an tsaro sun kwato shanu sama da 800 da ’yan fashin daji suka sace a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Bayanai sun nuna cewa gamayyar jami’an tsaron sun samu nasarar ce sakamakon wasu bayanan sirri da suka samu nasarar kwato shanun bayan sun yi ba-ta-kashi da barayin, wadanda suka gudu cikin daji suka bar shanun.

Kazalika, gungun maharan sun kai farmaki kauyen Biye da ke Karamar Hukumar Giwa inda suka sace mutane biyu a ranar Laraba da ta gabata.

Bayanan da Aminiya ta samu sun yi nuni da cewa maharan sun kai hari ne da misalin karfe 1:00 na dare.

Majiyarmu, wanda daya ne daga cikin jami’an tsaron da suka taimaka wajen kai farmakin wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan bindigar sun sami nasarar yin awon gaba da mutane biyun, inda daga nan suka kutsa kauyen Jabawa da ke Rugar Hussaini inda suka kora shanu guda 100.

Ya ce, daga nan ne suka shiga kauyen Danzan, Gidan Kosawa duk dai a Karamar Hukumar Giwa inda suka sace shanu guda 300.

Wakilin Aminiya ya gano cewa bayan sun shiga daji sai aka sanar da jami’an tsaro
inda suka bi sahun su, kuma bayan ba-ta-kashi na tsawon lokaci, jami’an tsaron suka sami nasarar kora maharan inda suka gudu suka bar shanun da suka sato.

Tuni ya ce har an mayar da shanun ga masu su bayan tsananta bincike.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandar Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar wa Aminiya hakan a yayin wani rangadin da suka yi da wakilin Aminiya a wani yankin na dajin Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.