Wasu da ake zargin jami’an tsaro ne sun kama Garkuwan Matasan Jihar Zamfara saboda shirin zanga-zangar da ke tafe kan tsadar rayuwa a Najeriya.
A wani bidiyo da ya tayar da kura a kafofin intanet, an ga Garkuwan Matasan Zamfara, mai suna Bashir jami’an tsaro sun sa masa ankwa a hannu suna dukan sa tare da barazanar hallaka shi.
A cikin bidiyon, an ji jami’an tsaron suna tursasa masa suna dukan sa cewa ya janye daga zanga-zangar, amma ya ce allambaran, “gaskiya ba zan janye ba.”
Jami’an tsaron, wadanda ba su bayyana fuskokinsu ba, sun tambaye shi dalilin zanga-zangar, inda ya bayyana musu cewa zaluncin ne dalili.
- DSS ta kama buhu 2,000 na shinkafar tallafin da aka karkatar a Katsina
- NAJERIYA A YAU: Shin Zanga-Zanga Kan Sauya Al’amura A Najeriya?
Matashin ya ci gaba da cewa, “Ni ne Garkuwan Matasan Zamfara domin sun dora alhakins a kaina.”
A yayin da daya daga cikin jami’an ke umartan dayan ya doki matashin sosai, an ji mai dukan na cewa.
Jami’in tsaro: Za ka janye ko ba za ka janye ba?
Bashir: Wallahi sai dai a kashe ni, ba zan janye ba.
Jami’in tsaro: Mene ne dalilin zanga-zangar?
Bashir: Saboda zaluncin da ake yi mana ya yi yawa.
Jami’i: Wane irin adalci ne gwamnati ba ta yi muku ba?
Bashir: Komai ba a yi mana ba…
Jami’in tsaro: Wallahi za mu ia kashe ka in ba ka jane ba.
Bashir: Sai dai ku kashe ne…
Jami’in tsaron ya ci gaba da ce wa Bashir: Za ka goge bidiyoyin da ka yi ko ba za ka goge ba?
Bashir: Wallahi sai dai a kashe ni…
Jami’in tsaro: Wane irin adalci ne gwamnati ba ta yi muku ba?
Bashir: Babu abin da gwamnati ta yi mana.
Jami’in tsaro: to ka janye zanga-zangar.
Bashir: Wallahi ban janye ta ba!
Jami’in tsaro: Ba za ka janye ba? Wallahi za ka iya rasa rayuwarka.
Bashir: Wallahi sai dai a kashe ni, ba zan janye ba.
Jami’in tsaro: Bidiyoyin da ka yi ka yada wa duniya, ka goge bidiyoyin nan?
Bashir: Wallahi ba zan goge gaskiya ba.
Jami’in saro: Za ka iya rasa rayuwarka a kan wannan.
Bashir: Wallahi sai dai a kashe ni.
Jami’in saro: Wallahi za mu kashe ka!
Bashir: Wallahi ranka dade sai dai a kashe ni.
Daga karshe dai suka cukwikwiye shi suka tafi da shi.
Kawo yanzu dai, hukumomi ba su ce komai game da lamarin ba.