’Yan fashin daji sun kona wasu gonakin masarar shida kafin a girbe su a kauyukan Kwaga da Unguwar Zako da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
Danyen aikin ’yan ta’addan ya girgiza al’ummar kauyukan, musamman masu gonakin da abin ya shafa, inda suka rika nuna alhini.
Wakilinmu ya ga bidiyon irin barnar da wutar da ’yan fashin dajin suka cinna ta yi a gonakin.
Daya daga cikin masu gonakin, Malam Kabiru Halilu Kwaga, ya shaida wa Aminiya cewa a bara ya noma buhu 160 na masara a gonar, kuma a bana yana kyautata zaton samun fiye da haka, amma maharan suka kona gonar.
- Lakurawa sun karɓe aikin sarakunan gargajiya —Bukarti
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Hana Lalata Turakun Rarraba Wutar Lantarki
- IPMAN da Dangote Sun cimma yarjejeniya kan fara dakon mai