More Podcasts
Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na ci gaba da tsananta, lamarin da ya sa wasu al’umma ke neman hanyoyin kare kansu.
Ɗaya daga cikin hanyoyin da wasu yankuna suka ɗauka shi ne yin yarjejeniya da ’yan bindiga da ke addabar su, domin samun zaman lafiya.
- NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya
- NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi
Shin yin sulhu da ’yan fashin daji ita ce mafita? Kuma yaya halin yankunan da suka ƙulla irin wannan yarjejeniya yake a yanzu?
Shirin NAJERIYA A YAU, zai yi duba kan yadda wasu al’umma ke ƙoƙarin tsira daga matsalar tsaro ta hanyar yarjejeniya da ’yan bindiga, da kuma irin tasirin da hakan ke haifarwa.
Domin sauke shirin, latsa nan