✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina

Rundunar ta yi musayar wuta cikin dare da maharan kafin samun nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta daƙile wani harin ’yan bindiga tare da ceto mutum 30 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Faskari.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani da ke yankin.

“Da misalin ƙarfe 1 na dare, muka samu rahoto cewa wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani inda suka sace mutum 30,” in ji sanarwar.

Bayan samun rahoton, jami’an tsaro sun kai ɗauki, inda suka yi wa maharan kwanton ɓauna, sannan suka yi musayar wuta da su.

DSP Sadiq, ya ce babu wanda ya ji rauni daga cikin waɗanda aka kuɓutar, kuma jami’an tsaro sun samu nasarar dawo da wasu dabbobin da maharan suka sace.