✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashin daji sun kashe ’yan uwan juna biyu a Kaduna

Har yanzu ana ganin motsin ’yan fashin dajin a yankunanmu.

’Yan fashin daji sun bindige wasu matasa ’yan uwan juna biyu a kauyen Gajere da ke gundumar Kutemeshi na Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da safiyar Juma’a a lokacin da suke aiki a cikin gonarsu.

Dan majalisa mai Wakiltar Kakangi Yahaya Musa, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kazalika, Kakangi ya ce ’yan bindigar sun kuma sace wasu manoma biyu a ranar Alhamis a garin Gwanda Mai Gyada a lokacin da suke noma.

“Eh, na samu labarin kisan domin an kira ni da safe an fada min. Bayan wadannan ma ’yan fashin dajin sun sace wasu manoma biyu a Gwanda mai Gyada a ranar Alhamis dinnan,” inji shi.

Ya ce a yanzu haka ana ganin motsin ’yan fashin dajin a yankunan Kuyello da Tabanni da Kutemeshi sai kuma Dogon Dawa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya bukaci a ba bashi lokaci ya bincika lamarin domin samun karin bayani amma har ya zuwa hada wannan lokacin.