✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe manan ’yan bindiga Sani Black da Kachalla Makore a Zamfara

An kashe ƙasurguman ’yan bindigar ne makonni bayan kashe Halilu Sububu a Jihar Zamfara.

Rahotanni na cewa an kashe wasu ƙarin ƙasurguman ’yan bindiga — Sani Black da Kachalla Makore— a Jihar Zamfara.

Gwamnatin Zamfara ce ta tabbatar da cewar hukumomin tsaro a jihar sun hallaka riƙaƙƙun ’yan bindigar da suke addabar jihar tare da yaransu.

Bayanai sun ce an ta’addan biyu sune ke da alhakin kai hare-haren ‘yan bindiga a yankin Ɗan Sadau da kewaye da kuma wasu sassan Karamar Hukumar Maru.

Mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Alhaji Mustapha Jafaru Kaura, ya ce a ranar Lahadin da ta gabata aka hallaka Sani Black a ƙauyen ’Yar Tasha yayin da a ranar Talata kuma Kachalla Makore ya yi gamo da ƙarshensa a ƙauyen Kunkeli duk a Ƙaramar Hukumar Maru.

Alhaji Kaura ya yi bayanin cewa an hallaka ’yan bindigar ne tare da wasu mayaƙansu 23 yayin wani hari na haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka kai da suka haɗa da sojoji da kuma Askarawan Zamfara.

“Bayan an kashe Sani Black a wani harin kwanton ɓauna a ƙauyen ’Yar Tasha a ranar Lahadi, 22 ga watan Satumba na bana, sai Kachalla Makore ya haɗa tawagar mayaƙansa a ranar Talata waɗanda suka nufi ƙauyen ’Yar Tasha domin ɗaukar fansa da kuma ɗauko gawar riƙaƙƙen ɗan bindiga da aka halaka, Sani Black.

“Sai dai ya yi rashin sa’a, inda shi ma jami’an tsaron suka yi masa kwanton ɓauna suka hallaka shi a ƙauyen Kunkeli.

“An kashe Sani Black tare da wasu mayaƙansa mutum takwas yayin da Makore ya yi gamo da nasa ƙarshen tare da mayaƙansa mutum 15.

Alhaji Kaura ya bayyana wannan lamari a matsayin wata gagarumar nasara yana mai jinjina wa jami’an tsaro tare da kiran da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen ’yan bindiga da suka addabi jihar.

Mai magana da yawun Gwamna Lawal Dare ya ce gwamnati za ta ci gaba da faɗi tashin ganin an ruɓanya nasarorin da ake samu da kuma bai wa jami’an tsaro duk wani goyon baya da suke buƙata wajen fatattakar ’yan bindiga a jihar.

Ya roƙi mazauna jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro da sahihan bayanai da za su taimaka wajen cafkewa ko kuma hallaka ’yan bindigar da suka addabe su.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan nasara dai na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin Nijeriya ta ɗaukai mataki na samar da wata rundunar Fansar Yamma, a tsakanin jihohin Sakkwato, da Kebbi da Zamfara da Katsina don kakkaɓe ’yan ta’adda daga yankin.

A makonnin da suka gabata ne rundunar ta halaka gawurtacen ɗan bindigar nan da ya addabi jihohin Zamfara, Sakkwato, Katsina da Kaduna, Halilu Sububu, da ƙarin wasu ’yan bindiga fiye da guda shida da suka addabi yankunan.