✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kara farashin wutar lantarki a Najeriya

NERC ta amince kamfanonin raba wutar su kara farashi daga 1 ga watan Satumba, 2021.

Hukumar Kayyade Farashin Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta amince wa kamfanonin wutar lantarki su kara farashi daga ranar Laraba 1 ga watan Satumba, 2021.

Aminiya ta gano cewa Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki 11 (DisCos) sun samu amincewar NERC kan karin farashin ne ta wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Eko (EKEDC) ya aike ga kwastomominsa a ranar 25 ga Agusta, 2021.

“Ana sanar da ku a hukumance cewa za a samu karin kudin wutar lantarki daga ranar 1 ga Satumba, 2021.

“An yi karin ne bisa umarnin da aka bayar a fadin kasa na aiwatar da Kudin Jadawalin Sabis (SBT) wanda hukumar da ke kula da mu (NERC) ta amince da shi,” inji sanarwar da Babban Manajan  Rage Asara na EKEDC, Olumide Anthony-Jerome, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce za a fara ganin karin farashin ne a kudin  wutar lantarkin watan Satumba, 2021 wanda za a fitar da ‘bill’ dinsa a watan Oktoba.

“Ga kwastomominmu masu amfani da tsarin shan wuta a cikin gida, sai su kara farashin daidai gwargwado don nuna sabon karin farashin kamar yadda NERC ta fitar,” inji shi.

Sanarwar ta ce sabon farashin zai fara aiki ne daga Satumba zuwa Disamba 2021.

– Sabon farashin

A karkashin sabon tsarin da aka amince da shi na Eko DisCo, kwastomomin da ke karkashin Band A marasa shan wuta sosai an yi musu karin N2 a kan kowane kilowatt, daga N54.08 zuwa N56.08 tare da alkawarin ba su wutar ta akalla awa 20 a kullun.

Kwastomomin MD1 a Band A kuma yanzu za su rika biyan N58.94 a kan kowane kilowatt maimakon N56.94 da suke biya a baya.

Kwastomomin da ke kan tsarin B da D da E su ma abin ya shafe su: Masu amfani da wuta a gidaje na R2S da C1S  da Masana’antu (D1S) wadanda suke biyan N26 a kan kowane kilowatta za su koma biyan N28.

– Ba da yawunmu ba —EKEDC

Amma daga baya kamfanin na EKEDC a cikin wata sanarwa da Shugabansa, Injiniya Adeoye Fadeyibi, ya fitar a ranar Asabar, ya bukaci kwastomomin kamfanin su yi watsi da maganar karin kudin, da cewa ba daga hukumar gudanarwar kamfanin ko shafinsa na intanet sakon ya fito ba.

“Muna shawartar abokan cinikinmu da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba hukumar gudanarwar kamfanin ta fitar ba, ko ba a shafin intanent na kamfanin aka wallafa ba,” inji shi.