’Yan sanda sun kama wani yaro mai shekara 16 da aka samu dauke da bindiga a wata makarantar boko a jihar Anambra.
Kakakin ’yan sandan a jihar, Haruna Muhammed, ya ce yaron yana cikin mutum 80 da rundunar ta kama bisa zargin ayyukna kungiyar asiri.
Ya ce an gurfanar da mutum 40 daga cikin mutanen a kotu, aka kuma sallami mutum 15 bayan an tantance su ba a same su da wani laifi ba.
Akwai kuma mutum 5 da aka sallama bisa sharadin ’yan sanda za su ci gaba da sanya ido a kansu sai kuma mutum 20 da ake ci gaba da bincike a kansu.
Haruna Muhammed ya ce an kwace tarin makamai da bindigogi da albarusai a hannun wadanda ake zargin.