✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ’yar shekara 54 kan safarar makamai a Yobe

’Yan sanda sun kama wata mata mai shekeru 54 kan da harsasai 350 a Jihar Yobe.

’Yan sanda sun kama wata mata mai shekeru 54 kan zargin ta da fasakwaurin harsashi guda 350 a Jihar Yobe.

Rundunar ’yan sandan jihar na zargin matar ne safarar makamai ba bisa ka’ida ba daga garin Buni Yadi zuwa Damaturu.

Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce dubun matar ta cika ne a Damaturu bayan  samun bayanan sirri a kan ayyukanta.

“An kama wata mota kirar Golf 3 kuma bayan bincike an gano harsasai guda 350 samfurin 7.62x39mm a boye a cikin kayan wadda ake zargin.

“A halin yanzu ana yi mata tambayoyi domin gano abokan cin mushenta da kuma manufarsu,” in ji shi.

Dungus ya ruwaito kwamishinan ’yan sanda na Jihar Yobe, Garba Ahmed, yana jaddada aniyarsa ta yaki da laifuka tare da kira ga jama’a su ci gaba da ba wa jami’an tsaro  hadin kai.