Wasu ’yan Najeriya sun shiga hannun hukumomi kasar Saudiyya kan zargin fataucin hodar Iblis da nauyinta ya kai kilogram 55.2 a kasar.
’Yan Najeriyar su biyar na cikin wasu mutum 11 da jami’an Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi ta Saudiyya suka kama da hodar Iblis sin a birnin Jidda na kasar.
Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta Saudiyya ta ce gungun wadanda ake zargin sun boye hodar Iblis din ne a wurare daban-daban domin kawar da hankalin jami’an tsaro.
Da yake bayanin, Manjo Marwan al-Hazmi, wanda shi ne kakakin shugaban hukumar, ya ce dubunsu ta cika a wani samame da jami’an hukumar suka kai kai musu.
- Za mu maye gurbin likitoci masu yajin aiki da na wucin-gadi —Gwamnati
- Yadda jama’a suka kashe barawon babur a ofishin ’yan sanda
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya (SPA) ta ce ’yan Najeriyar da aka kama, suna da takardun ziyarar kasar ne, wasu mutum hudu kuma mazauna a kasar ne, sauran biyun kuma bakin haure ne da suka shiga kasar ta barauniyar hanya.
Saudiyya na da tsauraran dokoki a kan ta’ammali da miyagun kwayoyi, inda ake yanke wa masu fasakwaurinsa hukuncin kisa.
Dillalansa da masu amfani da shi kuma akan daure su a gidan yari ko a yi musu tara mai tsanani ko kuma a kore su daga kasar.