✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu maye gurbin likitoci masu yajin aiki da na wucin-gadi —Gwamnati

Halin da yajin aikin likitoci ya jefa asibitoci a sassan Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar daukar ma’aikatan wucin gadi da kuma biyan su da albashin likitoci da suka shiga yajin aiki.

Ministan kwadago, Chris Ngige, ya yi barazanar maye gurbin likitocin da suka shiga yajin aiki da ma’aikatan wucin-gadi ne a yayin hirarsa da tashar talabijin ta Channels.

Ngige ya yi wannan barazana ce bayan a ranar Laraba Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa (NARD) ta shiga yajin aikin gargadi na kwana biyar kan wasu bukatunta da gwamnati ba ta ci ba.

Bukatun likitocin sun hada da ninka musu albashi sau biyu da ba su sabbin alawus-alawus da kuma biyan su albashin da suke bin bashi gami da alawus dinsu na samun horo.

Amma a martaninsa, Ngige, ya ce ba hakan ba zai yiwu ba, yana mai zargin kungiyar da tsaurin ido ga Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) wadda ke tattaunawa da Gwamnatin Tarayya a kan bukatun.

Ya ce, “Likitoci masu neman kwarewar nan sabbin likitoci ne kuma suna cikin NMA; Matasan likitoci ne da ke samun horon kwarewa.

“Tun da hadaddiyar uwar kungiyar ta NMA na tattaunawa da gwamnati a madadainsu, wannan abin da suke yi rahin mutunta NMA ne.

“Abin da suke kuka a kai ma, babu shi,” in ji ministan. 

Halin da asibitoci ke ciki

Yajin aikin gargadin na kwana biyar ya gurgunta harkoki a asibitoci a fadin Najeriya, inda a Asibitin Kasa da ke Abuja, ake kin duba marasa lafiya, in banda a bangaren ba da kulawar gaggawa ko tiyata

Duk da haka akwai mutanen da aka kwantar, kuma kakakin asibitin, Tayo Haastrup, ya shaida wakilinmu cewa za su duba irin kulawar da wadanda aka kwantar din suke bukata, sannan su sallami wasu daga cikinsu.

Haka kuma, ya ce yajin aikin ya sa dole asibitin ya rage yawan mutanen da zai kwantar saboda aikin ya yi wa manyan likitoci da ke aiki yawa.

Kano

A Asibitin Koyarwar na Aminu Kano da ke Jihar Kano ma haka abin yake, inda bayan marasa lafiya sun hallara domin ganin likita a ranar Laraba, aka sanar da su cewa sai da su hakura su koma gida

Wani magidanci da ya kai dansa asibitin, Umar Yahaya, ya ce, “Muna layi ana tsaka da duba marasa lafiya suka fito suka ce ba za su duba yara ba, mutum 20 kacal za su duba, daga nan su tashi.” 

Wata mata mai suna Safiya Iliyasu, wadda ta kai ‘yarta asibitin domin ganin likita, ta ce, “Ban san yadda zan yi ba, nan muke zuwa ganin likita ni da ‘ya’yana. Sun ce ko yara ba za su duba ba. Ga irin halin da ‘yata ke ciki.”

Shugaban kungiyar NARD reshen asibitin Malam Aminu Kano, Dokta Haruna Yakub, ya ce sun dakatar da aiki gaba daya bisa umarnin kungiyar.

Da aka tambaye shi ko sun damu da halin da yajin aikin ya jefa marasa lafiya, sai ya ce, duk da cewa sun damu, amma idan har ba a biya musu bukatarsu a dalilin yajin aikin ba, to tamkar an yi hutun jaki da kaya ne.

Ya ce hadarin cika wa likita aiki ya fi na yajin aiki, saboda mutane na iya zuwa asibitin kudi inda likita zai iya duba su.

Bauchi

A jihar Bauchi, marasa lafiya na gunguni kan yajin aikin likitocin a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU-TH). 

Wakilinmu da ya ziyarci asibitin ya lura cewa wasu ‘yan tsirarun ma’aikatan jinya ke duba marasa lafiya.

Mataimakin Shugaban kungiyar ARD na ATBU-TH, Ahmed Isa Suleiman, ya bukaci marasa lafiya su yi hakuri, amma ya ce kungiyar da hukumar gudanarwar asibitin sun yi wani tanadi domin ganin su.

Maiduguri

Yajin aikin ya jefa manyan likitoci cikin damuwa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda su da ma’aikatan jinya suka koma kula da marasa lafiya.

Daya daga cikin kwararrun likitocin ya shaida wakilinmu cewa yajin aikin ya zo a daidai lokacin da ake fama da bullar cututtuka saboda yanayin zafi a jihar.

Ya ce saboda haka sun fi mayar da hankali a kan wadanda rashin lafiyarsu ta yi tsanani, a yayin kuma da ‘yan uwa ke korafi game da abin da suka kira rashin kula a bangaren likitocin.

Shugaban kunigyar ARD a asibitin, Dokta Usman Abdullahi, ya ce mambobinsu sun bi umarnin kungiyar 100 bisa 100 na shiga yajin aiki, duk kuwa da cewa reshen shi ne mafi girma a Najeriya da likitoci masu neman kwarewa 270.. 

Jos

Shugaban kungiyar ARD a Jami’ar Jos (JUTH), Dokta Artu John, ya ce ba 100 bisa 100 aka samu bin umarnin a asibitin ba.

Duk da haka, yawancin mutanen da suka je ganin likita sun nuna damuwarsu, inda wani mai suna Othman Dauda ya ce, “Dole na je asibitin kudi, tun da na ji cewa yajin aikin na kwana biyar ne.”

Abin ya fi shawar marasa lafiya da aka kwantar a asibitin, domin kuwa likitoci ‘yan kalilan ke duba su.

Abeokuta

A Jihar Ogun, likitoci masu neman kwarewa a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da Babban Asibitin Kwakwalwa da ke Abeokuta sun shiga yajin aikin gadan-gadan.

Shugaban kungiyar ARD reshen Asibitin Kwakwalwa da ke Aro, Dokta Odubakun Kazeem, babu likitan da zai duba marasa lafiya a asibitin sakamakon yajin aikin.

A cewarsa, za a ci gaba da yajin aikin, har sai gwamnati ta biya bukatunsu.

Benin

A Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin da ke Jihar Edo ma (UBTH) ana yajin aikin, inda shugaban ARD na asibitin David Orhewere, babu ko mambansu daya da zai duba marasa lafiya a yayin yajin aikn, sai dai kwararrun likitoci su duba su.

“Ranar Lahadi za a sallami marasa lafiyar da yanayinsu bai yi tsanani ba; shi ma din manyan likitocin ne za su yi,” in ji shi.

Ya ce ba su jin dadin yajin aikin, amma da alama, shi ne kadai abin da ke iya jan hankalin gwamnati ta yi abin da ya kamata.

Fatakwal

Yajin aikin ya gurgunta al’amura a Asibitin Koyarwa na Jami’ar  Fatakwal (UPTH), inda wani wanda ya je asibitin, mai suna Lucky ya ce sai da ya yi awanni kafin ya ga wani likita daga cikin wadanda ke aiki a lokacin yajin aikin. 

Shugaban ARD reshen UPTH, Dr Onua Author, ya tabbatar da sun shiga yajin aikin, amma shugaban kula da lafiya na asibitin, Dokta Datonye Alasia, ya ce sun yi tanadi ta yadda ba za a rasa likitan da zai duba marasa lafiya gaba daya ba. 

Ibadan

 A asibitin koyarwa na Jami’ar Ibadan (UCH) ma duk kanwar ja ce, inda shugaban ARD a asibitin, Dokta Abiodun Ogundipe, ya ce marasa lafiya na kwashe awanni kafin su samu ganin likita saboda karancin likitoci a yayin yajin aikin.

Ya ce daukar matakan ya zama dole da nufin rage yawan ficewar likitoci daga Najeriya zuwa aiki a wasu kasashe.

Yobe ba su shi gaba

Amma a Jihar Yobe, NARD ba su shiga yajin aikin ba, inda shugabanta, Dokta Mai Bukar Kalli, ya ce bayan ganawarsu da sakataren gwamnatin jihar, Baba Mallam Wali, gwamnatin jihar na kokarin biyan akasarin bukatun likitocin musamm ta bangaren samar da kayan aiki na zamani da inganta yanayin aikinsu. 

Kalli ya ce matsayin jihar ta daya daga cikin wadanda ke farfadowa daga rikicin Boko Haram, shigarsu yajin aikin zai kara jefa bangaren lafiyar jihar da ke kokarin farfadowa cikin matsala.

Ya ce gwamnatin jihar ce ke daukar nauyin mafi yawan likitocin, don haka babu yadda za a yi su ce ta yi watsi da su, kamar sauran wuare.

Sakataren gwamantin jihar, ya ce matakin da kungiyar ta dauka a jihar zai taimaka wajen kare rayuka da kuma inganta bangaren lafiya.

 

Saga Sagir Kano Saleh da Ojoma Akor (Abuja), Hamisu K. Matazu (Maiduguri), Yusufu A. Idegu (Jos), Peter Moses (Abeokuta), Usman A. Bello (Benin), Victor Edozie (Port Harcourt), Adenike Kaffi (Ibadan), Clement A. Oloyede, Salim U. Ibrahim (Kano), Hassan Ibrahim (Bauchi) & Habibu I. Gimba (Damaturu)