Hukumar tsaron farin kaya (Civil Defenve) ta a jihar Zamfara ta kama wasu ’yan mata guda biyu ’yan uwan juna bisa zargin leken asiri ga ’yan bindigar da suka addabi jihar Zamfara.
Babban kwamandan hukumar a jihar Aliyu Alhaji Garba ya ce wasu jami’an su ne masu aikin sanya ido a kan kaiwa da komowa dake karamar hukumar Anka suka kama ’yan matan, wadanda ’yan asalin Jamhuriyar Nijar ne.
An kuma kama wani mai suna Shafiu wanda ake zargin shi ma yana yi wa ya bindigar leken asiri.
Dukkan su an yi nasarar cafke su ne lokacin da suke kokarin shiga dajin Kuru-kuru bisa gayyatar ’yan bindigar bayan samun wasu kwararan bayanan sirri a kan su.
Babban Kwamandan ya kara da cewa binciken da suka yi ya nuna cewa Shafiu yana hulda da wani kasugurmin mai satar shanu da ake kira “Shaho” a yankin .
“Su kuwa Binta da Balki abokan huldar wani dan bindiga ne da ake kira Jijji. kuma ya dade yana lalata da su duka biyun a wani daji dake yankin karamar hukumar ta Anka.
“Mun kuma gama binciken farko-farko za mu mika su ga wasu jami’an tsaro domin kara bincike,” inji shi.
Dukkan mutanen uku dai sun amsa laifin da suka aikata.
Ita Balki, ’yar shekara ashirin da haihuwa, ta shaida wa wakilin mu cewa ’yan bindigar kan yi lalata da su suna kuma biyan su kudaden da suka kama daga N3,000 zuwa N7,000.
“Mu kan yi amfani da kudin wajen sayen abinci da kuma wasu bukatun yau da kullum.
“Mun zo ne daga Kwanni ta Jamhuriyar Nijar”, inji ta.
Jihar Zamfara dai ta jima tana fama da matsalar ’yan bindiga wadda ta ki ci ta ki cinyewa.