✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama ’yan Boko Haram 13 a Kano

Mazauna wasu unguwanni a Jihar Kano sun firgita bayan samun rahoton kamen.

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cafke wasu mutum 13 da ake zargi ’yan kungiyar Boko Haram ne a wani samame da ta kai Unguwar Hotoro da ke Jihar Kano.

Wata sanarwa da rundunar da ta fitar da yammacin Lahadi a shafinta na Twitter, ta ce an kama mutanen ne a wani gida da ke yankin Filin Lazio a Unguwar.

Aminiya ta ruwaito cewa, an kama ababen zargin ne sakamakon fadada bincike da tattara bayanan sirri da zummar inganta tsaro a Jihar Kano.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da fadada bincike don ganin ta zakulo miyagun mutane masu fakewa cikin jama’a da manufar cutar da su.

Kazalika, rundunar ta nemi mazauna Unguwar Hotoro da kewaye a kan su ci gaba da al’amuransu ba tare da wata fargaba ba.

Haka kuma, rundunar sojin ta nemi mazauna da su ci gaba da sanya ido kan duk wata bakuwar fuska ko motsin da basu gamsu da shi ba.

Babu shakka rahoton wannan kamen ya dimauta mazauna unguwar da ma na sauran wasu unguwanni a Jihar Kano.

%d bloggers like this: