A Jihar Oyo, ’yan sanda sun kama mutum uku da suka yi garkuwa da jami’ai biyu na Hukumar Shirya Jarrabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC), suka karbi kudin fansa mai yawa kafin su mika su ga iyalansu.
Mutanen da aka kama masu suna Muhammed Kote da Muhammad Legi da Kire Babuga suna daga cikin Fulani 25 da wani mai suna Kire ya yi safararsu daga Jihar Zamfara inda suke aikata miyagun ayyuka a yankin Kishi da Igboho a Jihar Oyo.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Abiodun Odude shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake nuna mutum 30 da aka kama da zargin aikata laifuffuka daban-daban a jihar. Ya ce an kama mutanen ne a maboyarsu da ke tsohuwar National Park a garin Igbeti.
Aminiya ta zanta da mutanen uku inda kowanne ya tabbatar da karbar Naira dubu 20 daga cikin kudin fansa fiye da Naira miliyan daya da jagoransu Kire ya karba daga hannun iyalan jami’an hukumar ta WAEC su biyu. ’Yan sanda sun ce suna neman Kire ruwa a jallo bayan jagorantar matasan Fulani 25 da ya horar da su aikata miyagun ayyuka na fashi da makami da garkuwa da mutane.
Kwamishinan ya ce rundunar ta yi nasarar kama wani yaron motar tirela mai suna Oluwaseun Olayiwola, wanda ya kashe ubangidansa ya binne gawarsa a cikin daji, ya gudu da motar dauke da buhunan sukari na dangote da ya boye a wasu shaguna a garin Ibadan maimakon kai wa garin Benin.
Haka kuma ya nuna wata tsohuwar jami’ar ’yar sanda mai shekara 38 mai suna Ayobami Odunayo da aka taba kora daga aiki amma ta ci gaba da sanya kayansu tana tana karbar kudi daga hannun mutane.
Matar mai ’ya’ya biyu ta fashe da kuka a lokacin da take yi wa ’yan jarida bayani kan danyen aikinta. Kwamishinan kuma ya nuna wadansu mutanen da aka kama kan zargin fashi da makami da sauran miyagun ayyuka a jihar.
An nuna wa ’yan jarida makaman da suka hada da bindigogi da adduna da wukake da Keke-NAPEP guda 4 da babura 3 da dimbin kudi da suturu da kayan tsafi da aka samu a wurin mutanen da aka kama, wadanda ya ce za su gabatar da su a gaban kotu a matsayin shaida idan suka kammala bincike.