Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta ce ta samu nasarar kama wadansu ’yan fashi da makami su kimanin bakwai ciki har da tsohon dan kwallon kulob din Niger Tornadoes da ke Minna mai suna Nura Mohammed.
Tsohon dan kwallon da aka kama tare da abokan fashinsa ya bayyana wa ’yan sanda dalla-dalla yadda suke gudanar da fashi da makami a wurare daban-daban a fadin kasar nan.
Ya ce sune suka yi fashin wata mota kirar CRb Jeep da aka kerata a shekarar 2013 mallakar gidan talabijin mai zaman kansa na Channels.
Ya ce shi ya kasance mai sayen kayan da ’yan fashin suka sato ne musamman motoci, don a wasu lokuta ma a kasar Nijar yake kai kayan yana sayarwa an taba kama shi bayan ya ketara da wata mota kasar Nijar ya sayar da ita a can.
Ya ce ya taba buga wa kulob din Neger Tornadoes kwallo a shekarun baya inda kulob din ya rika biyansa albashin Naira dubu 150 a duk wata, amma raunin da ya samu a kafafunsa ne ta tilasta shi daina wasan kwallon kafa kuma ya bazama wasu Jihohi don neman abinci da hakan ta sa ya tsinci kansa a harkar fashi da makami.
Ya ce a Abuja ne a lokacin da ya bude gidan kallon kwallo ya hadu da wani makwabcin shagonsa mai sayar da lemon kwalba inda ya shigar da shi harkar saye da sayar da motocin sata inda dubunsu ta cika a yanzu bayan ’yan sanda sun samun nasarar kama su a Legas.
Nura dan shekara 33, mai da mata da yara biyu, ya ce an taba kama shi da laifin sayen motar sata a shekarar 2012 amma aka bayar da belinsa kuma bai daina sana’ar ba har aka sake kama shi a yanzu.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas Mista Kaytode Aderanti ya ce rundunarsa ta samu nasarar kama barayin ne a maboyarsu da ke Ikorodu a Jihar Legas.
Sauran ’yan fashin da aka kama su tare da Nura sun hada da Manben Bali dan kimanin shekara 40 da Cheikube Emaka dan shekara 32 da Ejike Chukwumeka dan shekara 37 da Jacob Ali mai shekara 28 da Titus Johana dan shekara 31 da kuma Richard Augusitine mai shekara 30.
Kwamishinan ya ce rundunarsa za ta tura su kotu da zarar ta kammala bincike don su fuskanci hukuncin da ya dace da su.