✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama tirela makare da naman jaki na N23m a Kebbi

An kama motocin makare da naman jaki da fatun jaki da ake shirin fitar wa kasashen waje.

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa (NSC) a Jihar Kebbi ta kama wata mota makare da naman jaki da fatun jaki da ake shirin jigilar su zuwa kasar waje ta garuruwan Kamba da yankin Maje da ke jihar.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Birnin Kebbi, Kwanturolan hukumar, Dokta Ben Oramalugo, ya ce mutanensa sun samu nasarar cafke naman jaki da fatun jaki da ake shirin yin safararsu daga kasar nan ta hanyar Bunza zuwa mahadar Maje a Jihar Kebbi, biyo bayan rahoton sirri da suka samu.

Ya ce naman jakunan da aka kama sun kai na sama da Naira miliyan 23.

Ya kara da cewa an kama mutum guda kan laifin safarar naman jakin.

Shugaban ya ce, “Mun yi wa jami’anmu cikakken bayani don kara sanya ido a kan hanyoyin da aka ambata.

“Kuma ta hanyar tsayawa da bincike jami’an sun samu nasarar cafke wata mota da ke dauke da naman jaki da fatu.

“Masu fasa-kwaurin sun lalata motocinmu guda biyu amma da taimakon wasu jami’an tsaro muka samu nasarar damke motocin da naman jaki da fatun, sannan an kama mutum guda,” in ji shi.

Ya ce sashe na 63 (b) na Dokar Hukumar Kwastam (CEMA) C45 LFN ta 2004, ya bai wa hukumar ikon kwace kayayyakin da ake shirin fasa-kwaurinsu zuwa kasashen waje.