Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da cafke wasu jami’anta biyu kan zargin azabtar da wani farar hula a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
Rundunar sojin a dibishin dinta na 6 da ke Ribas ce ta sanar da kama jami’an biyu bayan da wani bidiyo ya nuna suna azabtar da farar hula a jihar ta Ribas.
Bidiyon wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna wani sanye da kakin soji da kuma wani cikin kayan farar hula suna azabtar da wani mutum, duk da hakuri da ya yi ta ba su.
Mutumin ya yi ta kuka yana faɗin cewa: “A’a, don Allah ku yi hakuri, zan faɗi gaskiya.”
Wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta nuna ɓacin ranta kan abin da jami’an biyu suka aikata tana mai jaddada cewa ba za ta lamunci irin haka ba.
A sanarwar ta ranar Alhamis, Laftanar Kanar Danjuma Jonah Danjuma, mukaddashin kakakin rundunar, ya ce Kwamandansu Manjo-Janar Jamaal Abdulsalam, ya kuma ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
“Muna so mu tabbatar da cewa mun kama sojojin da suka aikata wannan abu na saɓa ka’idar aiki,” in ji sanarwar.
Sojojin sun tabbatar da cewa za su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da yin alkawarin hukunta waɗanda suka aikata laifin.
Mutane da dama sun yi Allah-wadai da abin da jami’an sojin suka aikata bayan da bidiyon ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda wani mai amfani da shafin X ya kwatanta ɗabi’un sojojin da “Rashin imani da kuma saɓa ka’idar aiki.”