Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kama wani kwamandan ’yan banga da ke dillancin miyagun kwayoyi.
Dubun kwamandan ’yan bangan ta cika ne bayan an kai samame a wata mashaya da yake gudanarwa, inda aka cafke wata budurwa da ke masa aikin sayar da kwayoyin, a garin Benin, Jihar Edo.
Kakakin NDLEA na kasa, Femi Babafemi, ya ce, hukumar ta kuma cafke wata budurwa mai shekaru 25 dauke da hodar iblis da kuma kwayar heroin a yankin Bagga da ke Jihar Borno.
An kuma kama maza biyu masu shekaru 25 da kuma 26 kowannensu dauke heroin da hodar Iblis a unguwannin Meri da Babban Layi da ke garin Maiduguri.
A Jihar Kebbi kuma, a babban tivin Jegga zuwa Sokkwato, an kama wani matashi dan shekaru 25 da dan shekaru 54 dauke da kwayoyi 44,820 na kodin za su kai Jihar Zamfara.
Dubun wani matashi shekaru 35 kuma ta cika, inda aka kama shi yana noma tabar wiwi a gonarsa ta tumatir a Karamar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna.
Su ma wasu mutum biyu dauke da sinki 99 na curarriyar tabar wiwi da suka dauko daga Legas za su kai Jihar Kano, amma dubunsu ta cika a Abuja.
Hukumar NDLEA ta kuma kuma wani dan shekaru 67 inda ta kwace tabar wiwi mai nauyin kilogram 57 kwaya 2,700 na tramadol da kuma kwalabe 231 na Kodin a hannunsu.
A yankin Anaca da ke Jihar Anambra, an kama wani dilan kwaya da kwalabe 483 na kodin da ya boye su a cikin wasu manyan jarkoki.
Sai Badagry da ke Jihar Legas inda jami’an hukumar suka kama kilogram 179 na wiwi.