✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kone gidan ƙaramar ministar Abuja

Gobarar ta tashi ne da tsakar ranar Lahadi.

Gobara ta kone Gidan Ƙaramar Ministar Babban Birnin Tarayya, Abuja Dokta Mariya Mahmoud.

Gobarar ta tashi ne a ranar Lahadi, inda ta kone gidan ministar.

Aminiya ta gano gobarar ta tashi ne gidan ministar da ke yankin Asokoro da tsakar rana.

Rahotanni sun bayyana cewar jami’an kashe gobara ba su kai dauki a kam lokaci ba, lamarin da ya sanya gobarar yin barna mai tarin yawa.

Duk da babu cikakken rahoto game da gobarar, amma hadimin ministar kan kafafen watsa labarai, Mista Austine Elemue, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai yi karin bayani ba.

Amma hadimin ya ce ana gudanar da bincike game da musababbin tashin gobarar a gidan ministar.