✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama mutumin da ya yi lalata da ’yar cikinsa a Legas

Mahaifin ya jima yana kai wa 'yar tasa hari.

Wata kotun majistare da ke Ikeja a Jihar Legas, ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai shekara 36 a yankin Roland Okajare, a gidan gyaran hali bisa zargin lalata da ’yarsa mai shekara 18.

Alkalin kotun, E. Kubeinje, wacce ta mika karar zuwa ga daraktan kararrakin jama’a na Jihar Legas (DPP), ta dage sauraren karar zuwa ranar 12 ga watan Afrilu.

Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, ASP Kehinde Ajayi, ya shaida wa kotun cewa Okajare ya aikata laifin ne a ranar 4 ga watan Janairu, a shagonsa da ke tashar mota ta Ikotun, Legas.

’Yar ta shi ta bayyana wa ’yan sanda yadda ya tilasta mata har sai da ya yi lalata da ita.

Sannan ta ce wannan ba shi ne karon farko da mahaifin nata ke kai mata hari ba.