✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 5 da ake zargi da yi wa Alkali dukan kawo wuka a Gombe

Mahara sun yi wa alkali da ma'aikatan kotu dukan kawo wuka kan rikicin fili a Gombe.

Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta samu nasarar kama wasu mutum 5 da ake zargi da yi wa wani alkalin wata Kotu da ma’aikatansa 3 dukan kawo wuka a yankin Putuki da ke kauyen Degri na Karamar Hukumar Balanga ta jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Yammacin wannan Lahadin.

Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe Hayatu Usman, ya bada umurnin a ci gaba da tsare wadanda ake zargin domin bin diddigin binciken.

Za mu dauki mataki kan harin da aka kai wa alkalin — Lauyoyi

Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) reshen Jihar Gombe ta lashi takobin ganin an hukunta wadanda suka kai wa alkalin babbar kotun jihar tare da ma’aikatansa hari suka sassare su.

Shugaban kungiyar a jihar, Barista Benjamin Sati, ya ce muddin irin haka na faruwa da akalai da ma’aikatan kotu, to kasar nan babu wanda zai tsira.

Sanarwar da ya fitar bayan harin da aka kai wa alkalin da ma’aikatan nasa da aka yi wa duka aka sassare shi, ta nuna rashin jin dadinsu kan wadanda suka yi masa wannan danyen aiki.

“Usman Yahaya, wanda ya ji mummunan rauni yana samun sauki, muna kira ga mambobin kungiyarmu da kada su fusata, su bai wa shugabani hadin kai wajen bin lamarin a hankali don cimma nasara,” in ji Sati.

Ya bukaci hadin kan dan sanda mai bincike na ofishin ’yan sanda da ke garin Talasse wanda zai sanar da ofishin kwamishinan ’yan sanda abin da ya faru ta hannun babban jami’i mai kula da sashen shari’a wanda yana cikin tawagar da suka kai ziyarar.

Yadda aka kai wa alkalin hari

Aminiya ta ruwaito cewa a makon jiya ne wasu bata-gari suka sassari alkalin wata Babbar Kotu ta III (UAC III) da ke Gombe, Ayuba Buba Dallas, da wasu ma’aikatan kotun uku a garin Degri da ke Karamar Hukumar Balanga ta Jihar Gombe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa sai da maharan suka yi wa alkalin da sauran mutane ukun kudan kawo wuka sannan suka sassare su.

Sauran wadanda lamarin ya shafa sun hada da wani lauya mai suna Barista Usman Yahya da wani ma’aikacin kotu.

Wata majiya ta ce wasu mutanen kauyen ne suka kai wa alkalin hari a lokacin da suke kokarin ganin sun warware matsalar rikicin wani fili.

Majiyar ta ce alkalin ya sha bugu ne daga kauyawan da ba a gane su wane ne ba a lokacin da shi da ma’aikatan kotun suka je duba filin a garin na Degri.

Wasu bayanai na alakanta harin da zargin da wasu ke wa ma’aikatan kotun da neman yin rashin adalci a takaddamar filin.