✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama mutum 3 kan yi wa mai gadi yankan rago a Taraba

An kama mutum 3 kan yi wa mai gadi yankan rago a Taraba

’Yan sanda sun kama wasu mutane uku a garin Takum da ke Jihar Taraba kan tuhumar su da laifin yi wa wani mai gadi yankan rago.

Marigayin, mai suna Jamilu Isa, yana gadi  ne a wani gidan sayar da man fetur a garin na Takum.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa wadanda ake zargin sun shiga gidan man da tsakar dare domin su saci man fetur, amma sai shi mai gadin ya gane su.

A cewar majiyar, barayin unguwar su daya ce da mai gadin wanda yasa ya gane su kuma ya ce zai tona asirinsu.

Jin haka ne sai barayi suka kama shi suka daure shi, sannan suka yi masa yankan rago.

Amma kuma sai wadannan barayin ta cika bayan sun kira wani mai mota ya yi masu dakon man fetur da suka sata suka boye a wani lungu da ke kusa da gidan man.

An ce direban ya tambaye su inda suka sami man fetur mai yawa haka amma suka kasa bayar da gamsasshen bayani.

Majiyar ta kuma shaida wa Aminiya cewa daga ne direba ya ce su bashi dan lokaci zai dauko wani amma su loda man a cikin motarsa daga kuma sulalai ya tafi ofishin yansanda ya tsaigudata masu.

Majiyar ta ce ba tare da bata lokaci ba ’yan sanda suka isa inda barayin ke jiran direban kuma suka kama su ukun.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Usman Abdullahi, ya ce ba su sami rahoton daga ofishinsu da ke Takum ba, amma zai kira DPO na yankin domin tabbatar da lamarin.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai i hakan ba.

%d bloggers like this: