Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Oyo, Mista Abiodun Odude ya ce rundunar ta kama mutane hudu da suka kashe kwamandan rundunar yaki da fashi da makami (SARS), ASP Shehu Magu.
Ya ce daya daga cikin mutanen da aka kama tun farko shi ne ya yi alkawarin nuna maboyar sauran mutanensa ga jami’an tsaron. A lokacin da kwamandan SARS Shehu Magu ya jagoranci tawagarsa zuwa dajin Ago-Amodu sai mutanen, wadanda dukkansu makiyaya ne, suka yi masu kwanton bauna suka kashe wannan jami’i.
An kama mutanen ne kwanaki biyu bayan aikata danyen aikin nasu, kamar yadda Kwamishina Odude ya bayya. “Za mu yi dukkan abin da muke iyawa wajen kamo sauran wadannan mutane da suka dade suna tayar da zaune tsaye a cikin garin Saki da sauran garuruwan Oke-Ogun a kusa da kan iyakar Najeriya da kasar Benin,” inji shi.
Kwamishinan ya fadi haka ne a yayin zantawa da ’yan jarida a Ibadan. Ya nuna wa ’yan jarida wasu mutane hudu da aka kama dauke da rubabben kokon kan mutum da kasusuwan hannaye da suka furta da bakinsu cewa suna yin tsafin samun kudi ne da wadannan sassa na jikin dan Adam. Alfa Hammed Sulaiman da Pastor Tope Akinyele sun yi wa ’yan jarida bayanin yadda suka guntile wadannan sassan jikin mutum daga wata gawa da suka tono daga wani kabari a Ibadan.
Haka kuma ya nuna wani matashi mai suna Alaba Ojo mai lakanin ‘Ojo Weli-Weli’ da aka kama bayan an dade ana nemansa ruwa a jallo a dalilin jagorantar ayarinsa na ’yan daba da suke kone-konen kadarori da kashe-kashen rayuka a birnin Ibadan.
Har ila yau, ya nuna wata babbar mota dauke da buhunan simintin dangote guda 863 masu darajar kudi fiye da Naira miliyan 4.4 da wasu mutane masu suna Ahmed Olagbemi da Lanre Adams da Akin Olorode da Hammad Abass suka damfari wani mai suna Rafi’u Ibrahim ta hanyar sayen wannan siminti da biyan kudin bogi a cikin banki. Ya ce duka mutanen da aka kama za a gurfanar da su gaban kotu ne bayan kammala bincike.