Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya (NAFDAC), ta cafke wasu mutum uku da ake zarginsu da sayar da gurbataccen sinadarin hada abin sha wanda ya yi sandiyar mutuwar mutum uku a Jihar Kano.
A ranar 11 ga watan watan Maris ne aka yi zargin wasu mutum uku sun mutum sanadiyar shan wasu nau’o’i na abin sha a Jihar Kano, wanda bincike ya nuna cewa suna dauke da sinadarai masu lahani ga lafiyar bil Adama.
- Za mu gabatar da tafsirai cikin yaruka daban-daban a Gombe — JIBWIS
- WAEC ta tabbatar da ranar fara jarrabawa a bana
Wata sanarwa da Kakakin Hukumar NAFDAC, Olusayo Akintola ya fitar, ta ce an samu nasarar kama ’yan kasuwa da ke da hannu a sayar da kayayyakin, sai dai ba a bayyana sunaye ko adadin wadanda aka kama ba.
Sanarwar ta ce Shugabar Hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ta gargadi ’yan Najeriya kan amfani da sinadaran karin dandano ko sauya launin abinci ko na sha, lamarin da ta ce na iya haddasa cututtuka ko mutuwa.
Hukumar ta ce ta aike da sakamakon binciken farko da ta yi a kan mutanen da lamarin ya ritsa da su zuwa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yayin ziyarar wuni biyu da suka kai jihar bayan faruwar al’amarin.
Farfesa Mojisola ta kuma yi nuni da cewa, ire-iren wannan hatsari na faruwa ne ta hanyar ci ko shan kayan abinci da suka lalace bayan karewar wa’adin da aka dibar musu na kasancewa masu aminci.