Jami’an hukumar tsaro ta NSCDC a Jihar Gombe sun kama wani matashi mai shekara 24 bisa zargin kwarewa wajen sayar da gurbataccen bakin mai ga masu ababen hawa.
Kwamandan hukumar a Jihar, Waziri Baba Goni, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya gabatar da wanda ake zargin a helkwatar hukumar.
- Kudurin mayar da Kwalejin Ilimi ta Bichi jami’a ya tsallake karatu na 2 a majalisa
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 47 a Borno
Ya ce sun kama matashin, mai suna Nuhu Umar, ne a lokacin da jami’ansu suka bad-da sawu bayan samun rahoto a kan shi.
Kwamandan, ya hori al’umma da su zama masu kula a lokacin da suka je sayen bakin mai don gudun sayen gurbatacce a hannun masu son zuciya.
Ya kuma ce jami’ansa suna ci gaba da ayyukan su yadda ya dace don kare al’ummar daga fadawa hannun irin wadannan mutane.
A cewar Kwamandan, tuni wanda ake tuhumar ya amsa laifin, inda ya ce ana kawo masa bakin man ne daga Jihar Kano.
Ya ce mutanen da ke son banza da yawa ne wajen neman sauki suka fi fadawa hannun irin wannan matashin.
Sai dai matashin ya bayyana nadamarsa, inda ya ce daga yanzu zai kiyaye ya zama mutum na gari
A nasa jawabi Shugaban masu sayar da bakin mai na Jihar Gombe karkashin kungiyar NUPENG, Hassan Bukar, ya ce kungiyar su ta ji dadin yadda aka kama shi aka kuma ji cewa daga wata Jihar aka shigo da shi, don haka matakin da aka dauka na dakile shi daga wannan mummunar sana’ar ya yi dai dai