✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matashin da ya kashe budurwarsa mai juna biyu a Kano

Ana ci gaba da bincike gabanin mika shi gaban kuliya.

Rundunar ’yan sanda Jihar Kano ta samu nasarar cafke wani matashi mai suna Philibus Ibrahim bisa zargin kashe budurwarsa mai juna biyu.

Bayanai sun ce ana zargin matashin ya kashe budurwarsa, Theresa Yakubu mai shekara 22 a duniya.

Kwamishinan rundunar ’yan sanda na jihar, CP mamman Dauda ne ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da manema labarai ranar Talata a Kano.

An kama Ibrahim ne a kan hanyar Gabriel Bila ta Karamar Hukumar Tudun Wada a Jihar Kano.

“A ranar, labari ya zo wa hukumar mu ta ’yan sanda cewa, an ga wata mata a kwance a gefen titi tana shure-shuren mutuwa a kan hanyar Kano zuwa Jos daidai kauyen Anadaria.

“Nan da nan jami’anmu mu suka hallara a wajen, aka kaita Babban Asibitin Tiga da ke karamar hukumar, wanda likitan ya baiyana ma cewa ta mutu.”

Kamar yadda bincike ya bayyana, Theresa ta baro Nasarawan Kuki zuwa ’Yan Tomo na Karamar Hukumar Garun Malan ta jihar a ranar 27 ga watan mayu, 2023.

Dauda, ya kuma kara cewa ana ci gaba da bincike gabanin mika shi gaban kuliya.