Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta yi nasarar kama wasu matasa biyu — Rabilu Adamu mai shekara 22 da ke zaune a garin Gombe Abba a Karamar Hukumar Dukku ta Jihar Gombe da Ado Yusuf mai shekara 28 da ke Kauyen Zoro na Karamar Hukumar Darazo ta Jihar Bauchi — kan zargin garkuwa da kisan yaro dan shekara 3.
Hakan na dauke ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar Yan Sandan Jihar Gombe ASP Mahid Mu’azu Abubakar ya fitar.
- Gaskiyar magana kan batun ‘rusa’ sashen Masallacin Abuja
- Mutum miliyan 283 ne suke kwana da yunwa a Afirka – Adesina
ASP Mahid ya bayyana cewa, a ranar 20 ga watan Oktoba 2023 wani mai suna Malam Sadi Musa da ke garin Gombe Abba ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na Dukku, inda ya sanar cewa a ranar 18 ga watan Oktoba da misalin karfe 12 na rana wasu sun sace masa dansa mai suna Isma’il Sadi dan shekara 3.
Ya ce daga baya mahaifin yaron ya fara zargin wani mai suna Rabilu Adamu da yake zaman Kawun yaron a kan shi ya sace dan nasa.
ASP Mahid, ya ce bayan samun rahoton ne suka tura jami’ansu inda abun ya faru kuma suka yi nasarar cafke shi wanda ake zargin domin amsa tambayoyi.
A cewar Kakakin, yayin amsa tambayoyi ne Rabilu ya amsa zargin da ake masa, inda ya ce shi ya sace Isma’il Sadi ya kuma mika shi ga wanda ya sa shi ya sato yaron, wato Ado Yusuf.
Sanarwar ta kara da cewa, tawagar ’yan sandan karkashin jagorancin Baturen ’Yan Sanda na Dukku da suka bazama, sun kamo Ado Yusuf inda ya ce yaron ba ya hannunsa kuma bai san inda aka kai shi ba.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, a yayin da aka ci gaba da titsiye matasan biyu ne suka amsa zargin sace yaron wanda suka ce sun daure shi a wani daji tun safe ba su waiwaye shi ba sai karfe 11 na dare, inda bayan sun koma suka tarar ya mutu sakamakon daurin da suka yi masa.
“Daga nan suka sanya gawarsa a cikin buhu suka kai shi dakin Rabilu, sai warinsa ya sa jama’a suka farga aka shiga bincike har rahoton ya zo gare mu.
“Jami’anmu sun mika gawar zuwa asibiti kuma aka tabbatar da ya mutu.”
A tattaunawa da wadanda ake zargin a shelkwatar ’yan sandan da ke Gombe, ababen zargin sun ce kaddara ce amma suna neman a yi musu sassauci.