Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wata matashiya mai shekaru 27, bisa zargin sheka wa wani matashi Lawan Inuwa Ibrahim, dan shekaru 25 tafasasshen ruwan shayi a jikinsa.
Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yayin ganawa da manema labarai a Juma’ar nan.
- Kotu ta umarci PDP ta sake zaben fidda dan takarar Gwamna a Zamfara
- ISWAP da Boko Haram sun kashe mayakansu 30
Ya bayyana cewa, rundunar ta samu korafi ne daga wasu mutane a unguwar Rimin Auzinawa da ke Karamar Hukumar Ungogo a ranar 11 ga watan Satumba.
Ya kara da cewa, “Bayan samun korafin ne rundunar ta tura jami’anta karkashin Baturan ’yan sanda na unguwar Rijiyar Zaki, CSP Usman Abdullahi, inda suka garzaya da matashin asibiti tare da cafke wadda ake zargin.”
“Bayan kai shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad ne aka kwantar da shi kuma likitoci suka shiga yi masa magani a fuska da hannunsa da kuma cikinsa, wuraren da ya samu kuna.
A nata bangaren, wacce ake zargi ta amsa cewa ta watsa masa ruwan kuma ta yi hakan ne sakamakon rikici da ya barke a tsakaninsu.
A cewarta, tana zargin matashin da kashe mata aure ta hanyar kai gulmace-gulmace wajen mijinta.
Matar ta ce matashin ne ya soma yunkurin sheka mata ruwan zafi a lokacin da kokawa ta kaure a tsakaninsu.