Sojoji sun danke wasu mata bakwai ’yan kungiyar Boko Haram tare da ceto mutum biyar da kungiyar ta yi gakuwa da su a Jihar Borno.
Wadannan mata mata da sojojin Bataliya ta 195 ta Operation Hadin Kai suka damke, dubunsu ta cika ne a yankin Maiduguri da ke Arewa maso Gabashin jihar.
- Yadda surukaina suka yi garkuwa da matata —Magidanci
- DAGA LARABA: Kamen ’Yan Arewa: Shin Lokacin Daina Ci-Rani Ya Yi?
Wani jami’in tsaro ya shaidawa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Yankin Tafkin Chadi cewa an kama matan ne da tarin kayan abinci da sauransu da za su kai wa mayakan kungiyar.
“A yayin binciken, an gano abubuwa daban-daban da suka hada da dumbin gidajen sauro da mai da taliyar yara da sauransu.
“An kuma gano gari mai tarin yawa da aka sanya a jarkoki aka boye a karkashin mota.
“Bayan an yi musu tambayoyi, matan sun amsa cewa su ’yan Boko Haram ne da ke aiki a sansanin gudun hijira na Muna Garage, Mafa da Dikwa da ke tare da mayakansu a Boboshe da Gulumba Riverline a karamar hukumar Dikwa.
“Sun bayyana cewa sun sanya garin a jarkoki ne domin su kauce wuraren bincike da kuma kare shi daga ruwan sama kamar sauran kayayyakinsu da ke binne a wuraren musayar da suka amince da su, inda mayakansu ke karbar su.
“Su kuma mutanen da aka yi garkuwa da su, sun ce mayakan na yin garkuwa da su ne bisa la’akari da yawan shanun da suka mallaka ko girman gonaki.
“Sun kuma sanar da sojojin cewa ana ba su kudi daga N50,000 zuwa N20,000 a kowace tafiya kuma suna tafiya kusan 2 zuwa 3 a rana.
Bayan wannan bayanin ne nan take sojojin suka fara kai samame sansanin na Boko Haram musamman a kusa da Gaza, inda aka kashe wani dan kungiyar guda daya.