’Yan sanda sun cafke ’yan bindiga mata biyu tare da gungun wani jagoran ’yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Abuja.
An kama matan ne tare da gungun wasu maza huɗu da ake addabar Abuja a maboyarsu da ’yan sanda suka kai samame.
Sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce wadanda ake zargin, ciki har da wani jagoran ’yan bindiga Buhari Muhammad, wanda ake nema ruwa a jallo, an kama su ne a wani otel da ke kauyen Bassa a Abuja.
SP Josephine Adeh, ta ce gungun ne suka yi garkuwa da wani Joshua Eze, wanda matarsa Blessing ta samu raunin harsashi a yayin da ake kokarin sace shi a ranar 27 ga watan Janairu, amma daga bisani ’yan sanda suka kubutar da shi ba lafiya washegarin.
- An yi jana’izar tsohon gwamnan Yobe Bukar Abba a Masallacin Harami
- An kama dan bindiga da shanun sata 55 a Kano
Sanarwar ta SP Josephine Adeh, kakakin rundunar ‘yan sandan, ta ce an kwato bindiga kirar AK47 guda daya, wayoyin hannu 10, kudi naira 345,000 da wasu kayayyaki masu daraja daga hannun wadanda ake zargin.
Ta kara da cewa tuni wadanda ake zargin suka amsa laifin da suka aikata da kuma wasu laifuka na garkuwa da mutane a yankin.
A cewar sanarwar, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, kwamishinan ’yan sandan Abuja, Benneth C. Igweh, ya tabbatar wa jama’a a kan kudirinsa na kawar masu aikata manyan laifuka daga Abuja.
Ta bukaci mazauna yankin da su bayar da rahoton abubuwan da ba su yarda da take-takensu ba ga wadannan layukan kar-ta-kwana 08032003913, 08061581938, 07057337653, da 08028940883; 0902222352.