An kamata wata mata da ta boye miyagun kwayoyi a al’aurarta a ya yin da take kokarin yin fasakwaurisu daga Najeriya zuwa kasar waje.
An cafke matar ce da kulli 18 na kwayoyin heroin da nauyinsu ya kai gram 234.35 da ta boye a cikin al’aurarta a safiyar Juma’a a hanyarta da zuwa kasar Italiya.
- An kama matar da ta kashe kishiyarta ta kona gawar
- Shin malaman Kano za su iya ja da Abduljabbar?
- Mun gano masu garkuwa da daliban Kaduna 39 —Gumi
- Yadda kayan hada rabobi ka sa kankancewar al’aura —Bincike
Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) sun damke matar ’yar asalin kasar Chadi ne a lokacin da ake auna fasinjoji kafin hau jirgin Ethiopian Airline zuwa Addis-Ababa, daga nan ya wuce Italiya.
Kakain NDLEA, Femi Babafemi, ya ce matar sana’ar gyaran gashi tun bayan komwarta kasar Italiya da zama a 2016, ta shaida ta ce wani ne daga can ya kira ta cewa ta kawo mishi kwayoyin kuma ya sa wani ya kai mata su dakin otel din da ta sauka a Legas.
“Ta ce mutumin ya kawo mata kulli 50 na kwayoyin heroin ta hadiya, amma ba za ta iya ba, shi ne ta cusa kulli 18 a cikin al’aurarta ta mayar wa mutumin ragowar,” kafin ta fito zuwa Abuja, inji shi.
Matar ta ce ta zo Najeriya domin samun kudin gida da shagon da take haya a Italiya, saboda hayan ya kare kuma harkoki sun dagule mata tun bayan bullar annobar COVID-19.
Babafemi ya ce matar ta ce mutumin da ya ba matar kwangilar fasakwaurin miyagun kwayoyin ya yi mata alkawarin biyan ta Yuro 10,000 idan ta kai masa su Italiya.