Rundunan ’Yan sandana Jihar Bauchi ta kama wadansu mutane da ake zargin sun shahara wajen satar babura ta hanyar zarge wuyan masu su da wayar kebur a Jihar Bauchi.
Kakakin Rundunar DSP Kamal Datti Abubakar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Bauchi, inda ya ce kame mutanen ya biyo bayan wani bincike ne da sashi na musamman da ke dakile fashi da makami a jihar ya yi. Ya ce sun kama Kamalu Mohammed mai shekara 27 da Tijjani Musa mai shekara 23da suke unguwanni Nasarawa da Bakaro a garin Bauchi, inda aka same su da babura biyu masu launin ja da mai ruwan toka da ake zargin na sata ne, kuma an same su da igiyar kebur da suke zarge wuyan wadanda za su kwace wa babur da wuka mai kaifi da mabudai masu bude kan kowane babur guda uku da sassan jikin babura da aka babballe. Ya ce an taba tsare su biyun bisa zargin fashi da makami da satar babur.
Haka rundunar ta kama wani da take zargin gawurtaccen barawon babur ne mai suna Abubakar Umar mai shekara 35 da ke kauyen Turum. Ya ce ana kan bincike in sun kammala za a kai su kotu.
Sai ya shawarci jama’a su kara bai wa ’yan sanda hadin kai domin a samu nasarar shawo kan aikata laifuffuka a jihar.