✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama masu yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

An tsare wasu sojoji bayan jami'an tsaron Fadar Shugaban Kasa sun dakile juyin mulkin

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dakile yunkurin sojoin kasar na yin juyin mulki a yin da ake gab da rantsar da sabon shugaban kasar.

Rahotanni daga Niamey, babban birnin kasar sun tabbatar cewan an tsare wasu sojoji da ake zargi da neman hambarar da Gwamnatin Shugaban Mahamadou Issoufou kwana biyu kafin rantsar da sabuwar gwamnati.

“An tsare wasu sojoji da ke da hannu a yunkurin juyin mulkin. Masu tsaron Fadar Shugaban Kasa sun mayar da martani, suka hana sojojin isa Fadar Shugaban Kasar,” inji wata majiyar tsaro.

Ta ce, “An ji rugugin harbi na kusan rabin awa a kusa da Fadar Shugaban Kasa amma jami’an tsaron Fadar Shugaban Kasa sun dakile yunkunin kuma yanzu komai ya lafa.

“Saura kwana biyu a rantsar da sabon Shugaban Kasa. Mun san babban kakulen da ke gabansa shi ne matsalar tsaro, abin da muke tunani shi ne harin ’yan ta’adda ba irin wannan ba.”

Tunda da karfe uku na asubahin ranar Laraba aka ji karar harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Kasar a birin na Niamey, yayin da ake shirye-shiryen rantsar da Shugaba mai jiran gado, Mohamed Bazoum.

Nijar na fama da hare-haren ’yan bindiga kamar sauran makwabtanta na yankin Sahel, inda kungiyar Boko Haram da kungiyar ISWAP da dangoginsu suke addaba.

Bayan zaben Bazoum wanda shi ne tsohon Ministan Harkokin Kasashen Waje, abokin karawarsa kuma tshon Shubagan Kasar, Mahamane Ousmane, wanda aka kayar a zagaye na biyu ya yi watsi da sakamakon bisa zargin an yi magudi.

A makon jiha Kotun Kolin kasar ta tabbatar da nasarar Bazoum, wanda shi ne dan lelen Shugaba Mahamadou Issoufou mai barin gado, wanda kuma zai kai ga rantsar da Bazoum din a matsayin Shugaban Kasa a ranar Juma’a, 2 ga Afilu.