’Yan sanda sun cafke wasu mutum bakwai da ke yi wa ’yan bindiga safarar man fetur da kayan abinci zuwa cikin daji a Jihar Katsina.
Mutanen da aka kama sun hada da mutm biyar masu sayar wa ’yan bindiga man fetur da mutum daya mai kai musu burodi sai kuma mai garkuwa da mutane.
- Sojoji sun dakile yunkurin juyin mulki a Sudan
- Yadda rikicin Boko Haram ya lakume rayukan yara 300,000 a Arewa maso Gabas
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce daga cikin wadanda aka kama har da wani matashi daga Jihar Maradi ta Jamhuriyar Nijar da aka kama ranar Asabar zai kai wa ’yan bindiga man fetur a daji.
Akwai kuma wani mai shekara 28 daga Magamar Jibiya da aka kama dauke da man shi ma zai kai wa bata-garin a cikin daji.
“Rundar ta kuma cakke wani dattijo mai shekara 50 daga kauyan Daddara a Karamar Hukumar Jibiya yana kai wa ’yan bindiga man fetur a cikin mota kirar Golf III.
“An kuma kama wani mai shekara 57 daga unguwar Kofar Guga yana kai musu man fetur.
“Dubunsu ta cika ne a kan hanyar Katsina zuwa Jibiya za su kai wa ’yan bindiga man fetur a ciki daji,” a cewar SP Isa.
“Da aka titsiye su a wurin bincike sun amsa cewa suna yi wa ’yan bindiga jigilar man fetur ne a yankin, sabanin dokar da aka kafa wacce ta hana yin hakana,” inji shi.
Akwai kuma wani mai shekara 25 a kauyen Anguwan Nakaba da ke Karamar Hukumar Sabuwa, da ke kai wa ’yan bindiga mai a cikin daji.
“An fara zargin daya daga cikinsu ne bayan an lura da yadda suke yawan zuwa gidajen mai suna sayen mai a wani gidan mai a kan babura a Karama Hukumar Dandume.
“Sai ’yan sandan leken asiri suka yi ta bin sahunsa, inda suka ritsa shi bayan ya shiga cikin wani kango inda yake juye man a cikin jarkoki.
“A wurin bincike ya amsa laifinsa, inda ya ce daga Karmar Hukuamr Sabuwa yake zuwa sayen man domin kai musu cikin daji.” inji shi.
An kuma kama wani mai shekara 30 daga Sabon Garin Motso, a Karamar Hukumar Jibiya da ke kai wa ’yan bindigar burodi yana kuma kai musu bayanai.
“Bayan sarakuna da hukumomin tsaro sun sha yi masa kashedi cewa ya daina ne aka kama shi a hanya dauke da burodi a cikin buhu zai shiga daji da su, shi ma ya amsa laifin da ake zargin sa.”