✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu garkuwa da mutane 11 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta sami nasarar kama mutane 11 da ake zargi da aikata yin garkuwa da mutane.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta sami nasarar kama mutane 11 da ake zargi da yin garkuwa da mutane.

Hakan na kunshe cikin sanarar da jami’in hulda da Jama’a na rundunar ’yan sandan, ASP Mansur Hassan ya fitar a ranar Alhamis,

Hassan ya ce an kuma samu bindigogin AK47 kirar gida guda 6 sai Pump Action Machine guda 2 da Fistol kirar Ingila guda 2 da Kuma wata bindiga kirar gida guda daya sai Kuma tsabar kudi Naira dubu 908,600 da sauran wasu kayayyakin.

A cewarsa kamen ya biyo bayan garkuwa da Hakimin a ranar 14 ga watan Agusta 2024 aka Kuma sako shi a ranar 16 ga watan Agusta 2024.

“A ranar Litini 2 ga watan Satumba 2024 ’yan sanda da ke yankin Saminaka tare da hadin gwiwar kungiyar Mafarauta suka Kai samame kauyuka uku a Karamar hukumar Lere, Maraban Wasa da Gurza Hakimin Mariri da Kuma Abugan Kurama.

“Wannan samamen sun yi nasarar kama mutane 5 sune Abdulhamid Abubakar Wanda akafi sani da A Mai shekara 30 da Danjuma Luka Wanda ake kira da UBA Mai shekara 25 da Ayuba Simon Mai shekara 50 da Kuma Idi Saleh Mai shekara 57.

“An same su da bindiga kirar gida guda daya da mota kirar Golf Mai launin ganye da Babur kirar Bajaj guda daya da kuma wayar hannu guda 8.

“Haka nan Kuma a ranar 2 ga watan Satumba 2024 da misalin karfe 9.00 na dare sun sami ingantaccen bayani game da kaiwa da komowar ’yan bindiga kuma ba tare da bata lokaci ba suka yi nasarar kama su a tashar mota.

“A lokacin da suke binciken kayan wadanda ake zargin sun kama bindiga guda AK47 guda uku kirar gida a cikin kayansu.

“Haka Kuma a wayewsr gari sun kama mutane 6 dake da nasaba da wadanda aka kama.

“An sami AK47 kirar gida guda 4 da Fistol kirar Ingila guda 2 da Pump Action Machine guda da kwanson harsasai guda 29.

“An Kuma sami tsumburkai da yawa a tare da su da wayar tafi da gidanka da Adda guda daya da kuma kudi Naira dubu 908.600.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa “ranar Talata 3 ga watan Satumba 2024 da misalin karfe 10 na dare sun sami bayanin cewar akwai wani da ake zargin Dan bindigane ya sauka a otel a yankin Tafa da ke Karamar hukumar Kagarko ba tare da bata lokaci ba suka Kai samame kuma suka yi nasarar kama wani mai suna Yahaya Yusuf Mai shekara 41 Dan asalin kauyen Kabo da ke Karamar hukumar Gurara a Jihar Neja.

“A yayin binciken wadanda ake zargin sun amsa zargin da ake masu na garkuwa da mutane da kuma satan shanu a Jihar Neja da Kaduna a yayin da aka same shi da waya kirar Techno guda daya.”

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ya bukaci al’umma da su ci gaba da ba Jami’an tsaro hadin kai da goyon baya domin samun nasarar kawar da mugayen iri daga cikin al’umma a Jihar da kasa baki daya.