✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai motar da aka samu AK-47 a ciki

Rundunar ta ce waɗanda ake zargin suna hannun hukuma, kuma ana gudanar da bincike a kansu.

Dakarun Runduna ta 6 ta Sojojin Najeriya da ke Jalingo a Jihar Taraba, sun kama wani mutum da aka samu bindiga ƙirar AK-47 a motarsa.

A ranar 5 ga watan Satumba, sojojin sun tare motar a kan hanyar Wukari zuwa Jalingo, inda suka gano bindigar tare da wasu kaya da aka ɓoye.

Mataimakin kakakin rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde, ya ce wanda ake zargin ya bayyana cewar ya aiki direban motar, wanda yanzu haka ya tsere.

Ya ce ya aiki direban ne daga ƙauyen Gindin Doruwa zuwa ƙaramar hukumar Wukari don kai makaman.

Ya ƙara da cewa an kama mutumin ne a garin Mutum Biyu, hedikwatar ƙaramar hukumar Gassol tare da wani direba mai Mallam Isah Ibrahim, wanda ake zargi wajen haɗa baki.

Dukkaninsu suna hannun hukuma, kuma ana ci gaba da tuhumarsu don gano wasu bayanai da za su taimaka wajen kama direban motar da ya tsere.