✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama magidanci ya je kwartanci wurin matar amininsa

An kama shi tsirara a wurin matar wadda kuma kanwa ce ga matarsa.

An cafke wani mutum tsirara bayan da ya je kwartanci a wurin matar amininsa a garin Modojia, Jihar Katsina.

Aminiya ta gano cewa mutumin da aminin nasa ya je kwartanci a wurin matarsa ma’aikaci ne a Jihar Zamfara amma dan asalin Katsina ne.

Majiyarmu ta ce, wanda ake zargin babu inda ba ya shiga a gidan abokin nasa, hasali ma, abokin ya damka wasu hidimomin gidansa a hannunsa.

Majiyar ta ce, matar abokin ta sha kai wa mijinta kara cewa abokin nasa yana tunkaro ta da wasu maganganun da ba su kamata ba, amma mijin bai yarda ba saboda ganin yadda suke da abokin.

An kama shi dumu-dumu

A karshe dai wanda ake zargin ya fada tarkon abokin, inda ya nuna ya yi tafiya.

Daga nan sai ita matar ta kira wanda ake zargin, ba tare da sanin cewa mijin na nan a boye a gidan ba, tare da wadansu makwabta don su zamo shaidu.

Wanda ake zargin ya shigo har ya yi tsirara da nufin zakke wa matar, a nan aka kama shi, kamar yadda Aminiya ta ga bidiyon da aka dauke shi.

A cikin bidiyon, mijin ya rika tambayar wanda ake zargin cewa me ya zo yi a gidansa?

Shi kuma wanda ake zargin ya amsa cewa ya zo neman matar abokin ne kuma ba wannan ranar ya fara zuwa ba, amma har zuwa wannan lokaci bai samu nasarar biyan bukatarsa ba.

Surukan juna ne

Sai dai kuma wani labarin da Aminiya ta samu daga wani makusancin mutanen biyu ya ce akwai sarkakiya a cikin lamarin.

Ya ce wanda ake zargin shi yake auren yayar matar da ake zargin ya je kwartanci a wurinta.

Hasali ma, mai zargin ya auri matarsa ne sanadiyar ganin ta a wajen ’yar uwarta — matar wanda ake zargi.

Aminiya ta tuntubi ’yan sanda a kan lamarin, sai dai mataimakin kakakin Rundunar ya ce ba su da labari, amma da zarar sun samu rahoton za su sanar.

Amma wata majiya ta bayyana cewa an shawo kan matsalar a gida ta hanyar hada ’yan uwan bangarorin biyu domin shiga tsakani.