Wata mata da ta hadiye horar iblis da nufin fasakwaurinsu zuwa kasar Saudiyya ta shiga hannu a filin jirgi a Kano.
Dubun matar ta cika ne a yayin da take shirin hawa jirgi zuwa Kasa Mai Tsarki daga filin jirgi na Malam Aminu Kano, inda aka gano cikinta akwai miyagun kwayoyi.
- An cafke jami’in gidan yari kan zargin luwadi da ƙaramin yaro a Gombe
- NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Batun Satar Mazakuta
Bayan jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) sun tsare matar mai shekaru 45, ta amsa cewa wasu ne suka ba ta hadiye.
Daga baya ta jagoranci jami’an hukumar zuwa wani gida a unguwar Fatawa, inda suka kama kulli 52 na hodar Iblis.
Kakakin NDLEA na kasa, Femi Babafemi ya ce nauyin hodar Iblis din ya kai gram 676.
Ya ce hukumar ta kuma kana wata ’yar shekara 31 da sinƙi na tabar wiwi guda 52 da nauyinsu ya kai kilogram 30 a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.
Babafemi ya kara da cewa hukumar ta kama wani mutum da kwayar dubu hamsin na Tramadol a kan hanyar Bauchi zuwa Gombe.
Sun kuma lalata gonakin tabar wiwi guda biyu da fadinsu ya haura hekta shida a jihohin Ogun da Edo, inda aka lalata fiye da ton 10 na tabar wiwi.
Jami’in ya ce hukumar na gudanar da bincike kan wadanda aka kama kwayoyin a hannunsu kafin gurfanar da su a kotu.