Rahotanni daga birnin Dabo sun bayyana cewa, an kama wani direban babur mai kafa uku wanda aka fi sani da Adaidaita-sahu, Abdullahi Baba-kura, kan zargin sace wa fasinjansa wayar salula.
Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa, jami’an Hukumar Kula da Rage Cunkoson Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA ne suka cafke Baba-kurakwanaki biyu bayan kotu ta ba da belinsa sakamakon aikata laifin kwacen waya.
- An sallamo Sarki Salman daga asibiti
- Firaministocin EU 3 sun ziyarci Kyiv yayin da hare-haren Rasha ke kara tsananta
Dubun Baba-kura ta cika ne a ranar Litinin, bayan da ya dauki wani fasinja, inda suna tsaka da tafiya, sai ya yaudare shi ya kashe babur din a zuwan ya samu matsala.
A kan haka ne ya kuma ce fasinjar ya taimaka masa, ashe a garin taimakon ne ya zura hannu ya zare wayar.
Bayan fasinjan ya farga ne sai ya kama shi da kokawa, lamarin da ya ja hankalin jami’an KAROTA, inda bayan sun ji ba’asi, sai su ka damke shi a kan titin hanyar Fadar Gwamnatin Kano.
Da hukumar na tuhumar sa, Baba-kura da bakinsa ya amsa aikata laifin, inda ya ce kwanaki biyu kenan da ba da belinsa a kotu.
Da ya ke jawabi a kan lamarin, kakakin KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar-Na’isa, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce da zarar sun kammala bincike, za a mika mai laifin ga rundunar ’yan sanda domin gurfanar da shi a kotu.