✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama dillalin miyagun kwayoyi a Kano

Jami’an Tsaro na ’Yan Bijilanti a Jihar Kano sun kama wani matashi mai suna Lawan Ahmad mai inkiyar Dan Wase da ake zargi da sayar…

Jami’an Tsaro na ’Yan Bijilanti a Jihar Kano sun kama wani matashi mai suna Lawan Ahmad mai inkiyar Dan Wase da ake zargi da sayar da muggan kwayoyi da kuma yi wa al’umma kwace a Kasuwar ’Yankaba.

An kama matashin ne a ranar Litinin da ta gabata biyo bayan korafe-korafen da al’ummar yankin suka yi inda suke zargin ’yan daba da ke yi wa jama’a kwace.

Jagoran Bjilanti da ke yankin mai suna Abdullahi Jaje Maje ya bayyana cewa ayyukan kwace da muggan laifuka da ake yi a Kasuwar ’Yankaba ya sa suka baza komarsu wanda ya sanya suka yi nasarar kama wanda ake zargi.

A zantawarsa da Aminiya wanda ake zargin Lawan Ahmad ya ce an kama shi ne da ‘Ja’ guda 20 da ‘Diyazafom’ kati 4 da tabar wiwi kulli 7 sai ‘Fara’ guda 20 da kuma ‘Alawa’ guda 1.