✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan kwallon Najeriya a Indiya

An kama wani dan kwallon Najeriya mai suna Ikenna da laifin safarar miyagun kwayoyi. Jami’an tsaron Indiya ne suka kama Ikenna kan safarar wata kwaya…

An kama wani dan kwallon Najeriya mai suna Ikenna da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Jami’an tsaron Indiya ne suka kama Ikenna kan safarar wata kwaya da aka haramta mai suna Crystal meth mai nauyin giram 10.

A lokacin da jami’an tsaron suka tsananta bincike, Ikenna ya tabbatar da shiga da kwayar daga Mumbai.  An ce wanda ake zargin yana zaune ne a Arewa maso Gabashin Delhi, kuma tun cikin shekarar 2013 yake zaune a Indiya ba bisa ka’ida ba.

Jami’in ’yan sanda, Atul Kumar Thakur, ya ce ’yan sanda a karkashin jagorancin ACP Gokulpuri Anuj Kumar sun kama wanda ake zargin ne da tsakar dare a kan hanyarsa ta zuwa wani otel da niyyar sayar da kwayar bayan an kyankyasa musu labari. Da suka tsananta bincike a kansa ne sai ya kai su gidansa da ke Unguwar Kardampuri a yankin Jyoti Nagar da ke Mumbai inda suka sake gano hodar ibilis mai nauyin giram 18 a boye a dakinsa.

Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna Ikenna, wanda tun farko ya shiga Indiya a matsayin dan kwallo, yana zaune a kasar ce tun a 2013 ba tare da biza ba, wanda hakan ya sa ya koma dillancin miyagun kwayoyi maimakon wasan kwallon kafa.

Ikenna  ya tabbatar wa ’yan sanda cewa ya je Indiya ne a matsayin dan kwallon kafa amma daga baya ya shiga wata kungiya da ke safarar miyagun kwayoyi saboda irin kudin da yake samu.

’Yan sanda sun ce za su gabatar da shi gaban kotu da zarar sun kammala bincike don a yanke masa hukunci.