Jami’an tsaro sun cafke wani dan kasar waje da ke shigowa Najeriya domin yin garkuwa da mutane.
’Yan sanda sun cafke mutumin, wanda dan asalin kasar Jamhuriyar Benin ne, a Dajin Kosubosu da ke Karamar Hukumar Baruten ta Jihar Kwara, dauke da muggan makamai da kuma tsabar kudi Naira miliyan 2.3.
- Zan iya kwada wa saurayina mari a kan ‘bestie’ — Budurwa
- Yadda ’yan bindiga suka sa garin Kaduna a tsakiya
“Wanda ake zargin ya amsa cewa shi dan wani gungun wasu masu garkuwa da mutane ne a tsakanin kasa da kasa da ke Jamhuriyar Benin,” a cewar sanarwar da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta fitar.
Sanarwar da kakakin rundunar, Ajayi Okasanmi, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa ’yan banga ne suka taimaka wajen cafke mutumin, wanda aka kwace wasu wayoyin hannu a hannunsa, a Dajin Kosubosu da ke Karamar Hukumar Baruten ta jihar.
Ya kara da cewa nan gaba za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya da zarar rundunar ta kammala bincike.