Hukumomi a kasar Malaysiya sun cafke wani dalibi dan Najeriya mai shekara 28 kan fataucin miyagun kwayoyi, kimanin wata uku bayan an zartar da hukuncin kisa a kan wata daliba ’yar Najeriya, Mary George, a kasar.
Dalibin da ya shiga hannun hukumomin kasar ta Malaysia a wannan karon an kama shi ne da kullin tabar wiwi da kwayar syabu wadanda kudinsu ya kai Naira miliyan 6.5, nauyinsu kuma kilogram 32.76.
Babban Jami’in Dan Sandan Binciken Miyagun Kwayoyi na yankin Selangor, Tahir Kassim, ya ce an kama dan Najeriyan ne bayan ya jefar da kunshin tabar wiwin da yake safara a lokacin da ya ga ’yan sanda.
“Jami’anmu sun yi nasarar kama shi, daga nan ya kai mu wani gida a Mentari Court inda kwayoyin ke ajiye; A nan ne muka samu kulli 20 na tabar wiwi da aka matse a ajiye cikin wata jaka, da wasu 13 kuma a cikin wata jakar. Dukkansu nauyinsu kilogram 32.42.”
Tahir ya ce dan Najeriyan ya kuma kai ’yan sanda wani gida inda aka samu kwalaye 20 na busasshen ganyen tabar wiwi da kuma gram 110 na kwayar syabu a cikin kwali biyar.
Ya ce wanda ake zargin na tsare a hannun ’yan sanda tun ranar 20 ga watan Agusta ana bincikar sa domin gurfanar da shi a gaban kotu kan laifin safarar miyagun kwayoyi, wanda a kasar Malaysiya ake yanke wa masu aikatawa hukuncin kisa.
A shekarar 2015 yawan ’yan Najeriya da ke jira a zartar musu da hukuncin da kisa a gidajen yarin kasar Malaysiya ya karu.
A watannin baya, an zartar wa wata ’yar Najeriya, Mary George, hukuncin kisa a Malaysiya, bayan kama ta da laifin safarar kwayar methamphetamine mai nauyin gram 765.9 a filin jirgin sama na Kuala Lumpur, babban birnin kasar, shekara hudu da suka gabata.
A shekarar 2020, Jakadan Najeriya a Malaysia, Bello ya shaida mana cewa ’yan Najeriya 10 ne ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa da aka yanke musu a kasar, baya ga wadansu da dama da ake tsare da su kan shiga kasar ba bisa ka’ida ba, da kuma safarar miyagun kwayoyi.