Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) ta dakatar da wasu dalibanta har sai abin da hali ya yi bisa zargin su da shiga kungiyar asiri a jami’ar.
Hukumar gudanawar FUDMA ta dakatar da daliban ne bayan rahoton tsaro da Mukaddashin Babban Jami’in Tsaro Jami’ar, Tanimu Dari Atiku ya gabatar.
- Jiragen sama ke kai wa ’yan bindiga makamai —Fadar Shugaban Kasa
- Jiragen yaki sun ragargaji ’yan bindiga a Kaduna
- Yadda ’yan bindiga suka kashe mijina wata daya da aurenmu
“Daliban sun hada da wani da ke karatun digiri na biyu a Sashen Nazarin Halayyar dan Adam da wasu biyu masu karatun digirin farko a fannin; sai mutum na hudu da ke digirinsa na farko a Kimiyyar Kwamfuta.
“An dakatar da daliban ne byan da aka tabbatar su mambobin kungiyoyin asiri daban-daban ne, har sai an kammala binciken tsaro na karshe,” inji sanarwar da ta fitar.
Sanarwa dauke da sa hannun Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’an FUDMA, Habibu Garba Matazu ta ce Shugaban Jami’ar (VC), Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi, ya amince da dakatarwar.
“Shugaban Jami’ar ya gargadi dalibai a kowane mataki da su guji duk wani nau’i na kungiyar asiri da sauran munanan halaye.
“Ya bayyana kungiyar asiri a matsayin babbar matsala da ke damun Shugabannin Jami’ar da duk mutanen kirki da masu bin doka da oda.
“Ya sake nanata cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani wanda aka samu dan kungiyar asiri a jami’ar ba,” inji sanarwar.